logo

HAUSA

Abin Bakin Ciki Ne Amurka Ta Yi biris Da Matsalar Jin Kai a Yankin Gaza

2024-01-02 10:50:46 CMG HAUSA

DAGA MINA

Kwanan baya, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da wani kuduri na samar da gudummawar jin kai a yankin Gaza. Hadaddiyar Daular Larabawa ta UAE ce ta gabatar da wannan kuduri, duk da cewa ainihin wannan kuduri na neman an tsagaita bude wuta a yankin cikin gaggawa kuma na dogon lokaci. Abin takaicin shi ne, Amurka ta ki amincewa da wannan kuduri, shi ya sa aka yi ta gyara shi, har an dage lokacin kada kuri’u har sau 4, a karshe kuma, an zartas da shi bisa gyarar cewa, za a tabbatar da aikin samar da agajin jin kai a yankin. A wani bangare kuwa, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya tattauna tare da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ta wayar tarho, sai dai bayan tattaunawar, ya bayyana wa manema labarai cewa, bai nemi Isra’ila da ta daina bude wuta ba a yayin tattaunawarsu.

Kawo yanzu, rikicin tsakanin Palasdinu da Isra’ila a wannan karo ya haddasa mutuwar fararen hula Palasdinawa fiye da dubu 20, yayin da mutane fiye da miliyan 1.9 suka rasa matsugunansu. Fararen hular Gaza na cikin matukar tashin hankali har suna cewa: “Babu wani wuri dake da tsaro a Gaza.”

Amurka dake ikirarin cewa, tana matukar son kare hakkin Bil Adama, amma me ya sa ta yi biris da mumunan yanayin da Palasdinawa suke ciki. Ihun bakin ciki da fararen hula na yankin Gaza suke yi da kukan kananan yara ya shaida yadda Amurka ta yi kunnen uwar shegu game da wannan batu wanda kuma ya zama abin bakin ciki. (Mai zane da rubutu: MINA)