logo

HAUSA

Shirin taimako na dōTERRA China na taimakawa Sinawa mata fita daga talauci da ba da gudunmuwa ga ci gaban yankunan karkara

2024-01-01 15:01:12 CMG Hausa


Rinin Fengxiang, ya matukar burge Ran Guangjin, malamar fasahar zane, a lokacin da ta gano fasahar ta gargajiya a shekarar 2012. Hakika, fasahar ta burge ta sosai da har ta yi burin gado da yayata ta. Sai kuma Ran ta yi sa’a, ta cimma burinta da taimakon shirin tallafi na kasar Sin na kamfanin dōTERRA, wato dōTERRA China Helping Hands Program.

A shekarar 2018 ne, gidauniyar raya harkokin mata ta kasar Sin CWDF da reshen kamfanin dōTERRA dake kasar Sin suka kaddamar da wannan shirin, wanda manufarsa ita ce karfafa gwiwar matan da suke son fara harkokin kasuwanci, musamman a yankunan karkara ta hanyar samar musu da jari da horo. Kuma shirin ya yi nasarar taimakawa mata tsayawa da kafarsu tare da inganta rayuwarsu.

Wata jami’ar reshen kamfanin dōTERRA dake kasar Sin, ta bayyanaa cewa, “idan muka zabi shirin da za mu ba tallafi, muna bayar da muhimmanci ga fasahohin hannu dake cikin jerin al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba na kasa, saboda irin wadannan ayyuka za su iya kare al’adun gargajiya tare da ba matan karkara damar yin aiki a gida da samun kudin shiga. Haka kuma, mun fi son shirye-shiryen da za su iya saukakawa mazauna karkara wahalhalun rayuwa. Aikin gona shi ne kashin bayan ci gaban ko wace kasa. Mun yi imanin cewa, matan karkara za su iya zama jagororin da za su samar da ci gaban aikin gona, kuma suna da matukar muhimmanci ga bunkasa yanayin yankunan karkara.” Shirin taimako na dōTERRA China Helping Hands Program, ya tallafawa harkokin kasuwanci na mata har 26 a larduna da birane da jihohi 10 na kasar Sin, ciki har da Yunnan da Guizhou da Guangxi. Kuma sama da mata 4,000 sun ci gajiyarsa.

Ran Guangjin, ‘yar asalin Huishui, wata gunduma a yankin Qiannan na kabilun Buyi da Miao mai cin gashin kai dake lardin Guizhou na kudu maso yammacin kasar Sin, ta karanci zanen fenti na gargajiya a jami’a. Kuma kafin ta fara nata kasuwanci, ta yi aikin koyarwa a wata kwalejin koyar da fasahohi ta lardin Guizhou.

Rinin da ake kira da Fengxiang, wata fasaha ce ta gargajiya da mutanen Huishui ke amfani da ita. Mutanen kan hada ruwan bishiyar liquidambar da ganyenta ke zama ja a lokacin kaka, da kitsen bauna domin samar da wani mai na musamman. Sai su yi amfani da man wajen zana siffofi kan yadi da burushi. Bayan an rina, an tafasa, yadin zai koma shudi da fararen siffofi. An sanya wannan fasaha cikin al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da aka yi gado na kasar Sin.

An san fasahar rini ta Fengxinag a matsayin “kayan gargajiya na Buyi da ba a bukatar tonowa daga kasa”, amma mutane kalilan ne suka san da shi. Ran ta bayyana cewa, “fasahar rini ta Fengxiang, tsohuwar fasaha ce, duk da cewa wasu da suka yi gadon suna yinta, har yanzu, daukaka gadon wannan fasaha daga zuriya zuwa zuriya ba ta da karfi.” Bayan Ran ta kware kan fasahar Fengxiang, sai ta yanke shawarar kafa kamfaninta a shekarar 2017.

Yadda ake hada mai na musamman da ake amfani da shi a rini na Fengxiang na da sarkakiya. Tun da babu wanda yake sayar da man a kasuwa, dole sai da Ran ta koyi yadda za ta hada man da kanta. Ta ziyarci masana fasahohin da dama, kuma ta yi ta gwada hada man sau da dama. Daga karshe kuma, ta kware wajen hadawar.

Ran ta yi amfani da duk damar da ta samu wajen yayata fasahar rini ta Fengxiang. A shekarar 2018, ta gabatar da fasahar yayin baje kolin sana’o’in gargajiya na Shenzhen na Sin karo na 14. Kuma yayin baje kolin, darajar kayayyakinta da aka saya, wadanda suka hada alamomin gargajiya da na zamani, ta kai yuan 100,000, kwatankwacin dala 14,286.

Ran ta koyar da fasahar rini ta Fengxiang ga dalibai da matan karkara a kyauta, domin samun kwararru masu fasahar. Kamfaninta ya dauki matan da suka kware a fasahar rinin, kuma matan na iya samar da kayayyaki ko a wajen aiki ko a gidajensu. Kamfaninta ya samar da guraben aikin yi ga mata sama da 200, haka kuma ya horar da mutane 1,000.

Tun daga 2018, Ran ta koyar da fasahar Fengxiang ga dalibai 600 yayin shirye-shirye daban-daban da aka yi domin yayata fasahar. Ran ta ce, “Duk da ba lallai ne daliban su gudanar da aikin da ya shafi rinin Fengxiang a nan gaba ba, zan ci gaba da koyarwa. Idan har dalibi daya zai gaji fasahar, to wannan nasara ce.”

Kyautata rayuwarta da ta ‘yan uwanta mata, shi ne burin Zhang Shulan, daraktar reshen kwamitin JKS dake kauyen Suoyishan na gundumar Shilin ta kabilar Yi mai cin gashin kanta dake lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin. Tun daga shekarar 2014, Zhang take jagorantar mata wajen noman laimar kwadi domin cimma burinta.

Saboda fari da hamada, mazauna Suoyishan sun dogara ne da noman masara domin samun kudin shigar da bai taka kara ya karya ba. A shekarar 2014, Zhang ta yanke shawarar fara sana’ar noman laimar kwadi. Bayan shekaru 3, ta samu gogewa, tare da samun damar taimakawa mata samun arziki ta hanyar noman laimar kwadi.

Sabo da noman laimar kwadi ba ya bukatar aiki mai yawa, haka kuma yana da lokacin da ake yinsa, dama ce mai kyau ga matan karkara. Zhang tana so ta fadada nomansa, ta yadda karin mata a kauyen za su iya shiga a dama da su. Sai dai, ba ta da jarin da ake bukata. A shekarar 2018, da taimakon gidauniyar CWDF da kungiyar mata ta gundumar Shilin, ta samu tallafi daga shirin taimako na kasar Sin na kamfanin dōTERRA, wato dōTERRA China Helping Hands Program. Da jarin da shirin ya samar, Zhang da wasu mata 10 suka kafa kungiyar hadaka ta noman laimar kwadi. A shekarar 2019, kungiyar hadakar ta karbi hayar fili mai kadada 1.3, inda aka gina rumfuna 8 irin na noman zamani wato Greenhouse domin noman laimar kwadi. Yanzu kungiyar na da mambobi 68.

Zhang na fatan shirin zai samarwa mambobin da fasahohi da kayayyakin aiki da suke bukata, haka kuma zai bude musu kofar kyautata rayuwarsu.

Domin taimakawa mata marasa abun yi cin gajiyar ci gaban tattalin arziki da al’adu na kauyen, shirin tallafi na kasar Sin na kamfanin dōTERRA, wato dōTERRA China Helping Hands Program na taimakawa shirye-shiryen mata da gano karfinsu, ba domin ba su damar amfana da shirin kadai ba, har ma da ba su damar bayar da gudunmuwarsu ga ci gaban yankunan karkara.

Daga taimakawa mata fita daga kangin talauci, da karfafa musu gwiwar fara kasuwanci da samun aikin yi, zuwa taimakawa mata bayar da gudunmuwa ga ci gaban yankunan karkara, tare da kyautata rayuwar mata, shirin dōTERRA China Helping Hands Program na kokarin tafiya da yanayin da ake ciki na karfafawa mata gwiwa. Za a samu karin Ran Guangjin da Zhang Shulan a nan gaba. (Kande Gao)