logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya tura wasu ministoci biyu zuwa jihar Filato bayan wani hari da aka sake kaiwa a ranar Asabar

2024-01-01 15:10:37 CMG Hausa

Karamin minista a ma’aikatar tsaron Najeriya Bello Matawalle tare da ministar ma’aikatar ayyukan jin kai Mrs Betta Edu sun kai ziyara jihar Filato bayan samun rahoton wani hari da aka sake kaiwa yankin karamar hukumar Bokkos.

Ministocin biyu sun kai ziyarar gaggawa ne jiya Lahadi 31 ga watan Disambar shekarar bara ta 2023 bisa umarnin shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, kuma suna tare ne yayin ziyarar tare da manyan hafsoshin rundunonin sojan kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

A dai ranar Asabar 30 ga watan Disambar bara ne wasu dauke da makamai suka kashe wani magidanci da dansa a wani sabon harin da ’yan bindigar suka kai wani kauyen dake yankin karamar hukumar Bokkos cikin dare.

Bayan fito na fito da ’yan kungiyar tsaron sa kai dake kauyen, an kashe daya daga cikin maharan yayin da raguwar kuma suka tsare.

Da yake zantawa da manema labarai, karamin ministan tsaron na tarayyar Najeriya Bello Matawalle ya yi alawadai da harin na ranar Asabar da ta gabata, inda ya ce hakika shugaban kasa ya damu matuka kuma tuni ya umarci jami’an tsaron soji da su hanzartar maganin wadannan ’yan ta’adda ta hanyar daukar hukunci mai tsanani a kansu.

Ita ma ministar ma’aikatar jin kai Mrs Betta Edu cewa ta yi gwamnatin tarayyar ta kammala shirye-shirye kawowa wadanda rikicin ya shafa tallafin kayayyaki da suka hada da katifu, barguna, tufafi da kuma kayan abinci.

“Za mu yi aiki kafada da kafada da sojojin wajen rabon kayan, kuma tawagarmu ta bada agaji za ta kasance a jihar Filato nan da wata guda, kuma muna da kyakkyawan fatan cewa za su kula da dawainiyar mutanen da rikicin ya yi sanadin barin muhallansu, a waje guda kuma muna kokarin sake tsugunar da su.” (Garba Abdullahi Bagwai)