logo

HAUSA

Burin Sin na kara jin dadin zaman jama’a ya dace da begen jama’ar kasa da kasa

2024-01-01 16:43:09 CMG Hausa

Shekarar da ta gabata, shekara ce da bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya farfado, bayan ta kyautata matakan dakile da kandagarkin cutar COVID-19, wadanda ta dauki shekaru 3 tana gudanar da su. Ko da yake an fuskanci matsaloli da dama, amma dukkan Sinawa sun yi kokari don ba da gudummawarsu.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada a cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekarar 2024, wato “Muna da babban burin da muke fatan cimmawa, burin da ke shafar kowa, wato za mu yi kokarin ganin al’ummar Sinawa na kara jin dadin zaman rayuwarsu”. Kara jin dadin zaman rayuwa shi ne babban burin kasar Sin, kana ya dace da begen jama’ar duniya baki daya.

Idan ana son jama’ar duniya su kara jin dadin zaman rayuwa, da farko ana bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kasar Sin ta yi kokari wajen gabatar da ra’ayinta kan daidaita rikicin Ukraine ta hanyar siyasa, da takardar daidaita rikicin dake tsakanin Palesdinu da Isra’ila, da tura jami’ai da dama don shiga tsakani kan daidaita rikicin, wanda ya samu amincewa daga kasa da kasa.

Bunkasuwa shi ne mabudin daidaita dukkan matsaloli. A cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, tattalin arzikin Sin ya karu da kashi 5.2 cikin 100 a rubu’i uku na farkon shekarar 2023 bisa na makamancin lokacin shekarar 2022, Sin ta kiyaye matsayinta na kasa mafi bayar da gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Kana Sin ta kafa dandalin hadin gwiwa da dama don more damar samun bunkasuwa tare da kasashen duniya.

Jama'a a fadin duniya suna rayuwa mai kyau, kuma suna fatan samun karin adalci a harkokin duniya. An gudanar da taron kolin Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya, da dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya karo na uku, da shigar da sabbin membobi a cikin BRICS, da ganawa a tsakanin shugabannin Sin da Amurka a San Francisco, kasar Sin ta yi kokarin kiyaye tsarin kasa da kasa, da raya karfin kasashe masu tasowa, da kuma ba da tabbaci da kwanciyar hankali ga duniyar dake fuskantar sauye-sauye da rikici.

A yayin da aka shiga sabuwar shekara, ba ma kawai Sin tana tunanin kanta kadai ba, har ma da duniya baki daya. A shekarar 2024, kasar Sin tana son hada kai da kasashen duniya wajen tinkarar kalubale da sa kaimi ga samun wadata tare. (Zainab)