logo

HAUSA

Babban sakataren MDD ya yabawa tawagar MINUSMA da ta kammala aikinta a Mali

2023-12-31 16:28:06 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar jin dadinsa ga tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali ko MINUSMA a takaice, a yayin da ta kammala janyewa daga kasar.

Babban jami'in MDD ya jaddada muhimmiyar rawar da tawagar ta taka, wajen karfafa shirin samar da zaman lafiya.

Guterres ya ce, tawagar ta taka rawa wajen tabbatar da ganin an mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a karkashin yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu ta shekarar 2015, da kuma goyon bayan mika mulki wanda zai kai ga tabbatar da dawo da ikon mulkin kasa.

Babban sakataren ya nuna matukar godiyarsa ga ma'aikatan tawagar MINUSMA. Yana mai cewa, an yaba musamman ga shugaban tawagar El-Ghassim Wane, saboda shugabanci na gari da ya nuna a cikin yanayi mai wahala.(Ibrahim)