logo

HAUSA

Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da kashe ’yan ta’adda 6,880 a tsakanin 2023

2023-12-31 15:30:47 CMG Hausa

Hedikwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da cewa, sojoji sun hallaka ’yan ta’adda har 6,880, sannan kuma ta kame wasu 6,970 daga watan Janairun wannan shekara ta 2023 zuwa yau.

Daraktan harkokin yada labaran hedikwatar tsaron Major Janaral Edward Buba ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake bayani ga manema labarai a birnin Abuja game da nasarorin da rundunar sojin Najeriya ta samu a shekarar 2023 a yakin da take yi da ’yan ta’adda da masu tada kayar baya a sassan kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Major Janaral Edward har ila yau ya ce, a shekarar da muke ban kwana da ita, dakarun tsaron Najeriya sun sami nasarar ceto mutane 4,488 wanda aka yi garkuwa da su. Sannan kuma sun kwato muggan makamai har 3,320, sai kuma alburusai guda 39,075 da suma suka sami kwatowa daga hannun ’yan ta’addan.

Haka kuma dakarun sojin na Najeriya sun sami nasarar kwato lita miliyan 100.3 na danyen mai sai lita miliyan 60.3 na tattacen mai a ayyukan da suka gudanar a tsawon shekara ta 2023.

Ha’ila yau kuma dakarun sun sami nasarar kwato shanun sata har 830 daga hannun barayin shanu a shiyyar arewa masu yammacin Najeriya.

A kan batun harin da aka kai kwanan nan kuwa a wasu kananan hukumomi dake jihar Plato, Major Janaral Edward Buba ya kare zargin da ake wa dakarun tsaron Najeriya bisa jinkiri na kai dauki gaggawa a lokacin da ake tsaka da wannan hare-hare.

“Yankunan kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi suna da fadin murabba’in kilomita 2, 315, kuma kananan hukumomi suna da sama da kauyuka 350, kuma da yawansu a warwatse suke ba hada ba, wanda tazarar dake tsakanin wadannan kauyuka da sansanin soji ya haura kilomita 90.”

Daga karshe ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da hadin kai ga dakarun tsaron Najeriya, inda ya danganta wadannan nasarori bisa irin gudumawar da jama’a ke bayar a kai a kai. (Garba Abdullahi Bagwai)