Dan kasuwar kasar Najeriya dake gudanar da cinikayya a birnin Yiwu
2023-12-30 03:00:04 CMG Hausa
Dan kasuwa daga tarayyar Najeriya Kalu Orji, ya samu damar gudanar da cinikayya a kasuwar kananan kayayyaki dake garin Yiwu na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. Wannan kasuwa, wadda ke da kusan dukkan nau’o’in kayayyaki, ba ta taba bata masa rai ba. Kalu ya san dabarar yin mu’ammala da ’yan kasuwar kasar Sin, wato samun aminci ta hanyar kirki da biyan kudi nan da nan, wannan shi ma dalili ne na samun nasarar cinikayyarsa. Hanyar da ya bi wajen gudanar da cinikayya tana da sauki da kuma amfani, wato sayen kayayyaki daga garin Yiwu, sai jigilarsu zuwa kasashen Afirka don sayarwa. Kalu yana da wani makasudi, wato samun dalar Amurka miliyan 2 a shekarar 2024. (Safiyah Ma)