Kamfanin gine-gine na kasar Sin TEC ya kaddamar da fara aikin gadoji a cikin birnin Kano
2023-12-30 15:40:42 CMG Hausa
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci kaddamar da fara aikin gadojin sama da na kasa a cikin birnin Kano, wanda zai ci tsabar kudi har Naira biliyan 27.
A lokacin da yake kaddamar da ayyukan guda biyu, injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, an kirkiro da yin gadojin ne domin rage cunkoson ababen hawa da saukakawa jama’a wahalhalun sufuri a cikin birni.
Daga tarayya Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. //////
Gwamnan na jihar Kano ya ce, baya ga rage cunkoso, yin gadojin zai taimakawa fafutukar da gwamnati ke yi wajen rage gurbatar yanayi a jihar baki daya.
Injiniya Abba Kabir Yusuf ya nanata kudurin gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa ga al’umma wanda daya ne daga cikin ribar da ake samu a tsarin mulki irin na dimokradiyya. Ya ce, jihar Kano da take da mafi yawan jama’a a Najeriya tana bukatar karin ababen more rayuwa musamman tituna da ruwan sha da kuma asibitoci.
Mun zakulo ’yan kwangila wadanda suke da ma sanannu ne, kwararru ne marasa almundahhana ne wajen aiki, daya daga cikin wadannan ’yan kwangila shi ne kamfanin TEC Nigeria Limited wanda ba sa wasa da lokaci ko kuma inganci na aiki. Ina son na gayawa al’umma wannan aikin, aiki ne wanda za mu yi shi na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da kananan hukumomi 44, da ma abun da ake yi ko a gwamnatocin baya shi ne a yi hadin gwiwa.”
Ana sa ran dai zuwa karshen shekara ta 2024 kamfanin na TEC zai tabbatar da kammaluwar ayyukan, tuni kuma aka dakatar da al’umma daga bin wuraren da aikin zai gudana. (Garba Abdullahi Bagwai)