logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a yi kokarin tsagaita bude wuta tsakanin Palesdinu da Isra’ila

2023-12-30 17:02:03 CMG Hausa

Zaunannen mataimakin wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi jawabi a taron kwamitin tsaron majalisar kan batun Palesdinu da Isra’ila, inda ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su taimakawa burin tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu.

Jami’in ya ce, bayan sama da kwanaki 80 da barkewar sabon zagayen rikicin Palesdinu da Isra’ila, fararen-hula sama da miliyan 2 a zirin Gaza, na fama da mummunan bala’in jin-kai, da ba’a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Ya ce an zartas kudurori da dama a zauren babban taron MDD, gami da kwamitin tsaron majalisar, inda aka bukaci a tsagaita bude wuta, da kawo karshen azabtar da fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a Gaza, da bukatar bangaren da ya mamaye yankin ya girmama dokokin kasa da kasa, da dokokin jin-kai na duniya, amma abun takaici, har yanzu ana ci gaba da yi wa zirin Gaza kawanya, da hallaka ko muzgunawa fararen-hula, tare kuma da kara kai farmakin ba-zata, da kame a yankin yamma da kogin Jordan.

Jami’in ya kara da cewa, kamata ya yi sassan kasa da kasa su yi kokari tare, don tsagaita bude kofa, da sassauta illolin masifa, da kuma ceto rayuka. Kasar Sin ta kuma bukaci Isra’ila da ta dakatar da kai farmakin soja ba tare da bata lokaci ba, da kawo karshen azabtar da daukacin al’ummar zirin Gaza, da samar da duk wani sharadin da ya wajaba ga hukumomin jin-kai, don su bada tallafi a Gaza. (Murtala Zhang)