logo

HAUSA

Afirka ta kudu ta gurfanar da Isra’ila gaban kotun ICJ game da zargin kisan kiyashi a Gaza

2023-12-30 17:28:44 CMG

Mahukuntan Afirka ta kudu, sun shigar da kasar Isra’ila kara, gaban kotun kasa da kasa karkashin MDD, wato International Court of Justice a Turance(ICJ), game da zargin kisan kiyashi a zirin Gaza.

Afirka ta kudu, wanda ta gabatar da zargin a jiya Juma’a, ta zargi Isra’ila da yin watsi da nauyin dake wuyan ta, na kare yarjejeniyar dokokin yaki da kisan kiyashi ta MDD, bisa matakai da take aiwatarwa kan falasdinawa a zirin Gaza, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin wata sanarwa da ICJn ta rabawa manema labarai.

Cikin korafin, Afirka ta kudu ta bukaci MDD ta dauki matakan da suka wajaba, na dakile kara tabarbarewar halin da ake ciki, da dakatar da illata hakkokin falasdinawa, karkashin dokokin yaki da kisan kiyashi. (Saminu Alhassan)