logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da kwangilar gina kamfanonin casar shinkafa a wasu jihohi 10 na kasar

2023-12-29 09:23:36 CMG Hausa

Ministan harkokin noma da samar da abinci na tarayyar Najeriya Sanata Abubakar Kyari ya tabbatar da cewa, gwamnati ta bayar da kwangilar samar da kamfanonin casar shinkafa a wasu jihohi 10 dake kasar ciki har da birnin Abuja.

Ministan ya tabbatar da hakan ne jiya Alhamis lokacin da yake duba daya daga cikin kamfanonin da yanzu haka yake daf da fara aiki a garin Suleja ta jihar Naija, wanda kuma aka tsara zai rinka samar da tan 200 na chasassar shinkafa a kowacce rana.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministan ya ce, an samar da kamfanonin casar shinkafar ne karkashin Shirin gwamnati na hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu.

Sanata Abubakar Kyari ya ce, manufar hadin gwiwa dai shi ne domin a janyo hankulan masu saka jari ’yan kasashen wajen ta yadda za a bunkasa noman shinkafa a cikin gida.

Ya ce, a baya dai Najeriya ta dogara ne da shigo da shinkafa daga waje amma yanzu ta lura cewa za a iya sarrafa shinkafar da za ta iya maye gurbin ta waje da a baya aka dogara da ita.

Mininstan harkokin gonar na tarayyar Najeriya ya bayyana gamsuwa bisa yadda aikin kamfanin shinkafar dake Suleja ya gudana cikin nasara, inda ya kara da cewa, “Dorewar wannan kamfani dai shi ne gudanar da aiki a kai a kai, muddin dai ana samarwa kamfanin samfaretar shinkafa, to akwai tabbacin cewar zai dore, a sabo da haka akwai bukatar a kara ninka kokari wajen yin noma mai yawan gaske.”

Ya tabbatar da cewa, gwamnati a shirye take ta kashe ko da nawa ne a harkar noman shinkafa, musamman ma wadda ake samarwa a lokacin noman rani. (Garba Abdullahi Bagwai)