logo

HAUSA

Tawagar MINUSMA ta kammala aikinta a Timbuktun kasar Mali

2023-12-29 09:58:10 CMG Hausa

A jiya ne, tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali (MINUSMA) ta kammala aikinta a yankin Timbuktu na kasar Mali.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya bayyana cewa, aikin tawagar ya kare ne, bayan tafiyar jami'anta na karshe, wadanda suka tashi ta jiragen sama da na kasa.

Bikin mika ragamar aikin da ya gudana karkashin jagorancin gwamnan Timbuktu, Bakoun Kante, da Anton Antchev, daraktan tsare-tsare na tawagar, kana jami'in kula da harkokin gudanarwar MINUSMA, ya nuna a hukumance yadda aka mika sansanin MINUSMA na Timbuktu ga gwamnatin rikon kwarya ta Mali. Matakin dake nuna cewa, an mika sansanin a cikakken yanayin aiki.

Kakakin ya ce, wannan taron yana nuna rufe kashin farko na sansanonin MINUSMA guda uku da aka shirya. Idan ba a manta ba, tun a watan Yuli ne, tawagar ta janye kusan sojoji 1,867 da ’yan sanda 173, da kuma fararen hula 226 daga Timbuktu, kamar yadda kudirin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2690 ya umarta. (Ibrahim Yaya)