logo

HAUSA

Shugaban Somaliya ya sha alwashin zage damtse wajen yaki da ta'addanci a shekarar 2024

2023-12-29 09:59:06 CMG Hausa

Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya ce gwamnatinsa za ta zafafa yaki da ’yan ta'addar kungiyar Al-Shabab a shekarar 2024.

Shugaban wanda ke jawabi a wajen wani taro da aka gudanar a Mogadishu, babban birnin kasar a yammacin Larabar nan, ya bayyana kwarin gwiwa kan jami'an tsaron kasar bisa kokarin da suke yi na tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Taron jama’ar da aka shirya, wanda aka watsa kai tsaye ta kafafen sada zumunta, ya kuma baiwa shugaban kasar damar amsa tambayoyi daga ’yan kasar, kan sabbin batutuwan da suka shafi siyasa, da tattalin arziki da kuma tsaro.

Shugaba Mohamud ya ce, an kammala kashi na farko na aikin da kasar ke gudanarwa na fatattakar ’yan ta'addar Al-Shabab. Yana mai cewa, gwamnati na shirya kafa dakaru na musamman, domin tabbatar da nasarorin da aka cimma a yankunan da aka kwato daga hannun ’yan ta’adda.

Shugaban kasar wanda ya sha alwashin yaki da kungiyar al-Shabab ya ce, jami'an tsaron Somaliya sun nuna kwarewa, da da'a, da aminci a duk lokacin da ake fuskantar kalubale da barazana.

Mohamud ya kuma yaba da rawar da tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Afirka dake Somalia ke takawa, wanda ya ce ta samar da zaman lafiya da shugabanci a Somalia ta hanyar yakar 'yan ta'addar Al-Shabab. (Ibrahim Yaya)