Managartan Tunanin Sinawa: Zaman jituwa yana haifar da kowane abu
2023-12-29 09:53:10 CMG Hausa
"Zaman jituwa yana haifar da kowane abu, yayin da duk abubuwa suka kasance iri daya kuma kamar su daya, to abubuwa suna mutuwa ne kawai." Wannan yana nuna zurfin tsohuwar fahimtar Sinawa game da bambancin abubuwa. Ta yaya wayewar kan kasar Sin ta raya irin wannan gagarumin yanayi na hada kai? A cikin kashi na hudu na shirin "Managartan Tunanin Sinawa" mai gabatar da shirin ya fara shirin a farkon tsohuwar hanyar siliki, birnin Xi'an mai tarihi, tare da matashiyar masaniya Madam Xiang Shuchen.