logo

HAUSA

Matsalar tsaro ta sanya a sake rufe wasu kasuwannin sayar da shanu guda 11 a jihar Zamfara

2023-12-28 09:26:50 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta sanar da rufe karin wasu kasuwannin sayar da shanu har guda 11 dake sassan jihar daban daban.

Gwamnatin ta sanar da daukar wannan mataki ne jiya Laraba 27 ga wata cikin wata sanarwar da kwamashinan yada labaran jihar Alhaji Munnir Haidara ya rabawa manema labarai a garin Gusau, inda ya ce, gwamnati ta samu bayanan sirri dake nuna yadda yan ta’adda dake satar shanu ke amfani da irin wadannan kasuwanni wajen sayar da shanu.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Kasuwannin da aka rufe dai kamar yadda sanarwa ta bayyana suna yankunan kananan hukumomin Tsafe da Talatar Mafara da Anka da Maradun da Shinkafi da kuma Birnin Magaji.

Kwamashina na yada labaran ya ce, ya zamarwa gwamnati wajibi ta dakatar da hada-hada a kasuwanni a matsayin daya daga cikin matakan kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar baki daya.

“Mun samu rahotannin na sirri na cewa, ana hada-hadar shanun sata a wuraren, shi ya sa gwamnati ta dauki wannan mataki, hakkin gwamnati ne ta kula da kare rayuka da dukiyar al’umma, saboda haka mutanen wadannan yankuna da abun ya shafa su yi hakuri, gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin ta kara kare rayukansu da dukiyarsu, don haka da zarar an gama bincike kuma al’amura suka daidaita wadannan kasuwanni duka za a bude su ba da dadewa ba.”

Kwamashinan haka zalika ya ce, tuni gwamnati ta baiwa jami’an tsaro izinin kama duk wanda ya karya wannan doka ta zuwa kasuwannin da aka rufe. (Garba Abdullahi Bagwai)