logo

HAUSA

Amurka ta ba Ukraine kunshin makamai na karshe a wannan shekara

2023-12-28 14:31:54 CMG Hausa

A jiya ne, ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta sanar da shirin karshe na taimakon makamai da kayan aiki da za ta baiwa kasar Ukraine a wannan shekara, a daidai lokacin da gwamnatin Biden ke fama da matsalar karancin kudi a halin yanzu.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, darajar kunshin tallafin makamai da kayan aikin, sun kai dalar Amurka miliyan 250, kuma an samar da su ne a karkashin wasu tsare-tsare da aka tsara a baya game da samar da tallafin ga kasar ta Ukraine,

Kunshin taimako irin wannan da aka sanar, yana karkashin umarnin shugaban kasa ne, wanda ya ba da damar samar da makamai kai tsaye daga rumbun ajiyar makaman ma'aikatar tsaro, ta yadda za a iya kai su Ukraine cikin sauri.

Amurka dai ta riga ta yi amfani da kudade daga wani nau'i na samar da taimako ga Ukraine, shirin taimakon tsaron Ukraine da majalisar ta amince da shi, ya baiwa ma'aikatar tsaro damar sayan makamai ga Kiev, ta hanyar sanya hannu kan kwangila tare da masu kera makamai.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana a jiya cewa, tun lokacin da rikicin Rasha da Ukraine ya barke a watan Fabrairun 2022, Amurka ta kashe sama da dala biliyan 44.2 a matsayin taimakon soji ga Ukraine. (Ibrahim Yaya)