logo

HAUSA

Wasannin hunturu na kara bunkasa a kasar Sin bayan kammalar gasar Olympics ta Beijing ta shekarar 2022

2023-12-28 20:39:07 CMG Hausa

Shekarar nan ta bana, wato shekara guda bayan kammala gasar Olympic ta lokacin hunturu da birnin Beijing ya karbi bakunci a bara, shekara ce da harkokin wasannin hunturu ke kara samun tagomashi musamman yankin arewacin kasar, har ma da yankunan kudanci masu dumi.

Wannan kyakkyawan tarihi da gasar ta Olympic ta bari, ya ingiza habakar tattalin arzikin mazauna yankunan da ake gudanar da wasannin na hunturu, tare da sanya kasar Sin zama cibiyar duniya ta wasannin hunturu.

Tun daga tsakiyar watan Nuwamba ne dai aka fara gudanar da gasannin kasa da kasa a birnin Beijing, wadanda suka dawo da tunani na lokacin gudanar gasar Olympic ta 2022.

Hukumar wasan zamiyar kankara ta “National Speed Skating Oval”, ta samu yabo bisa yadda ta shirya gasar zamiya mafi sauri, sakamakon yanayin filayen zamiya mai inganci da ta yi amfani da su wajen gudanar da gasar ISU ta kasa da kasa ta shekarar 2023 zuwa 2024 a watan Nuwamba, yayin da cibiyar zamiyar kankara ta Beijing dake karkarar Yanqing ta shirya wasannin “bobsleigh”, da “skeleton” na kasa kasa a lokaci guda.

Har ila yau, a wurin shakatawa na Shougang dake Beijing, inda aka gudanar da bangare na gasar wasannin hunturu ta 2022, an gudanar da wasannin zamiya na “FIS Snowboard”, da “Freeski Big Air” tsakanin 30 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamban nan.

Yayin gasar ISU ta kasa da kasa ta shekarar 2023 zuwa 2024, tauraron wasan zamiyar kankara na kasar Sin Su Yiming ya yi rawar gani, inda ya lashe matsayin farko na gasar a karo na 2.

Bayan lashe gasar, Su ya ce "Wannan ne mafarin mafarki na. Yanayin na da matukar kyau. Abun farin ciki ne ganin yadda mutane ke kara sani da shiga a dama da su a wasannin hunturu"

Bayan hakan da mako guda kuma, sai aka bude gasar “FIS Freeski Halfpipe” ta kasa da kasa a Chongli. Kuma kamar yadda aka yi tsammani, zakarar gasar Olympic na Sin Gu Ailing, ta nuna bajimta, inda ta lashe lambar yabo ta gasar, har ma ta ce "Dawowa nan, da shiga ta gasa a karon farko a wannan lambun shakatawa bayan watanni 11, wani mafarki ne da ya zama gaskiya".

Gasannin “ISU” na gudun kankara na gajeren zango da “Grand Prix of Figure Skating”, sun gudana ne tsakanin 7 zuwa 10 ga watan Disamban nan, kuma da su ne aka kawo karshen wa’adin wata guda da aka shafe ana gudanar da gasannin kasa da kasa na hunturu a sassan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin.

Can a kudancin kasar kuwa, biranen Chongqing da Shanghai, sun karbi bakuncin gasannin zamiyar kankara daban daban, wanda hakan ke nuni ga yadda wasannin hunturu ke kara karade sassan kasar Sin.

A daya bangaren kuma, birnin Harbin ya cimma nasarar karbar bakuncin gasar wannin hunturu na Asiya na shekarar 2025, da kuma wannan ci gaba, Sin ta karfafa matsayin ta na babbar cibiyar wasannin hunturu a shekaru dake tafe.

Game da yadda gasar ISU ta gudana, daya daga wadanda suka kalli gasar mai suna Zhang ya ce "Ina da matukar sha’awar tseren zamiyar kankara na gajeren zango, don haka na je kallon gasar da ‘da na domin shi ma ya kashe kwarkwatar idanun sa. A gani na wasanni hanya ce mafi dacewa ta ilmantarwa a duniya, kuma ina fatan ‘da na zai samu karsashi daga kwazon tawagogin ‘yan wasa".

A ranar 25 ga watan Nuwamba da ya gabata, wurin wasan kankara na Chongli ya karbi bakuncin mutane 6,600, adadin da shi ne mafi yawa da wurin ya karba a rana guda, tun bude shi a shekarar 2012.

Shi kuwa wurin wasan kankara na Yabuli dake lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin, wanda aka bude ranar 9 ga watan Nuwamba, ya samu baki masu halartarsa a kullum wajen 5,500, inda a ranar da ya fi karbar baki ya samu mutane 7,500, adadin da ya haura wanda aka taba samu daidai lokacin a shekarar bara.

Sakamakon wasannin hunturu, wurare da dama a kasar Sin wadanda a baya duniya ba ta san da su ba, a yanzu suna kara zama wuraren zamiyar kankara. Ga misali birnin Altay na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake arewa maso yammacin kasar Sin, ya na kan gaba a jerin irin wadannan wurare, domin kuwa birnin na da filayen wasan kankara guda 3, wato tsaunin Jiangjun, da Koktokay da Jikepulin, wadanda ke da yankunan zamiyar kankara nau’o’i daban daban, da kuma lokuta daban daban na gudanar da wasan.

Wasu alkaluma da kamfanin hidimar tafiye-tafiye na Ctrip ya fitar, sun nuna karuwar masu nuna sha’awar wasannin zamiyar kankara a Xinjiang, inda wasannin suka samu karin kaso 155 bisa dari na adadin, yayin da wuraren shakatawa na kankara suka samu karin kaso 128 bisa dari na masu nuna sha’awar ziyartar su.

Yang Yang, wadda ta lashe lambar yabo a gasar Olympic ta lokacin hunturu da ya gabata, wadda kuma a yanzu ke matsayin mataimakiyar shugaban hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari, ta lura da yadda ake samun karuwar matasa dake shiga wasannin hunturu tun bayan gasar 2022.

A cewar Yang, "Gasar Olympics ta lokacin hunturu da Sin ta karbi bakunci ya daga matsayin Sin a idon duniya a wannan fanni, tare da gabatarwa ‘yan kasar nau’o’in wasannin kankara daban daban. Da wannan tushe, ko shakka ba bu zai haifar da bunkasar wasannin hunturu yadda ya kamata".

Albarkacin rufaffun dakunan wasannin kankara da ake da su, yanzu haka wasannin na kara samun karbuwa a yankunan kudancin kasar Sin. A karon farko a tarihi, yankunan Guangdong da Chongqing sun kafa kungiyoyin su na wasannin hunturu, da nufin shiga a dama da su yayin gasar kasa ta hunturu da za a yi a shekarar 2024. Tuni dai karuwar masu sha’awar wasannin kankara a Sin ya haifar da bunkasar masana’antun wasan tare da samar da sabbi da karin guraben ayyukan yi a fannin.

Wata takardar bayani da aka fitar game da wasannin zamiyar kankara a kasar Sin, adadin wuraren da ake gudanar da wasannin cikin shekaru 10, sun karu daga 200 zuwa sama da 700. A shekarar 2014, akwai rufaffun dakunan wasannin kankara 5 kacal a kasar Sin; amma ya zuwa shekarar 2023 yawan su ya karu zuwa sama da 50.

A shekarar 2020, Li Qun, wanda dan Asalin yankin arewa maso gabashin Sin ne, ya karbi aikin horas da ‘yan wasan zamiyar kankara a filin  Guangzhou Bonski Resort dake lardin Guangdong.

A cewar Li Qun, "Masu sha’awar wasannin sun kunshi yara, har zuwa ‘yan sama da shekaru 60, kuma ba wai bukatar su ita ce su koyi wasan zamiya kadai ba ne, har ma akwai masu son kwarewa sosai a wasan. Rufaffen wurin wasan kankara yana bayar da damar ci gaba da nishadi duk tsawon shekara, kuma hakan ne ya sa na zabi zuwa Guangzhou."

Ya zuwa shekarar 2025, an yi hasashen cewa, sashen wasannin hunturu na Sin zai kai darajar yuan tiriliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 140.

Game da hakan, mataimakin babban shugaban kamfanin “Asia Digital Group”, wanda ya tsara baje kolin kasa da kasa game da gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing Zhang Li, ya ce "Lura da saurin ci gaban da ake samu yanzu, musamman in an dubi rahoton dake cewa masana’antar za ta kai darajar kudin Sin yuan biliyan 890 a shekarar nan ta 2023, tabbas ya zuwa 2025 za ta kai darajar tiriliyan daya".