Harin dakarun Isra’ila ya hallaka mutum 20 a kudancin Gaza
2023-12-28 10:14:00 CMG Hausa
Wani harin bam da dakarun sojin Isra’ila suka kai kan wani gini mai kunshe da gidajen jama’a a garin Khan Younis, kusa da asibitin Al Amal dake kudancin Gaza ya hallaka a kalla mutane 20, tare da jikkata wasu gwammai.
Cikin wata sanarwar da ya fitar, kakakin ma’aikatar lafiya a Gaza Ashraf al-Qedra, ya ce adadin wadanda suka rasu na iya karuwa bayan harin na jiya Laraba. Al-Qedra ya ce, ana ci gaba da zakulo mutane daga baraguzan ginin da bam din ya fadawa.
Wasu shaidun gani da ido sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, akwai Falasdinawa da suka rasa matsugunansu da dama cikin ginin, yayin da bam din ya fada kansa.
Gabanin aukuwar harin, adadin wadanda hare-haren sojojin Isra’ila suka hallaka a zirin Gaza ya karu zuwa mutum 21,110, baya ga mutane 55,243 da suka jikkata, kamar dai yadda ma’aikatar lafiyar ta bayyana.
Cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an hallaka mutane 195, tare da garzayawa da wasu mutane 325 zuwa asibiti, sakamakon raunuka da suka ji biyowa bayan hare-haren sojojin na Isra’ila.
Game da hakan, Al-Qedra ya yi gargadi game da kaiwa mutane hari da gangan a yankunan dake daura da asibitin Nasser dake Khan Younis a kudancin Gaza, yana mai kira ga sassan kasa da kasa da su gaggauta daukar matakan da suka kamata, na tabbatar da ba da kariya ga asibitin, da ma’aikatansa, da wadanda ke jinya a cikinsa, da ma dubban masu neman mafaka dake zaune cikinsa. (Saminu Alhassan)