logo

HAUSA

Kowa Ya Gyara Ya Sani

2023-12-27 17:24:49 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana kudurinta na ci gaba da yin hadin gwiwa tare da dukkan bangarori, da kuma ba da himma da daukar matakai masu ma'ana a kwamitin sulhu na MDD, domin kawo karshen tashin hankali a zirin Gaza, da aiwatar da hanyoyin warware shirin kafa kasashe biyu, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta bayyana hake, a lokacin da take karin haske kan kuduri mai lamba 2720 da kwamitin sulhu na MDD ya amince da shi game da rikicin Palasdawa da Isra’ila, inda ta yi kira da a dauki matakin gaggawa na fadada ayyukan jin kai a zirin Gaza da samar da yanayi mai dorewa da kawo karshen tashin hankali.

Idan ba a manta ba, kasar Sin ta kada kuri'ar amincewa da kuduri mai lamba 2720, wanda shi ne kuduri na biyu da kwamitin sulhun ya amince da shi tun barkewar rikicin Falasdinu da Isra'ila. Ta kuma bayyana cewa, kudurin bai zo daidai da yadda kasashen duniya suke tsammani ba kuma yana da wasu gibi da ya kamata a cike su.

A yayin da ya zuwa yanzu rikicin Falasdinu da Isra'ila ya yi sanadiyar mutuwa da raunata dubban fararen hula, kana kuma yanayin jin kai a Gaza ke ci gaba da tabarbarewa, Sin ta bukaci da a aiwatar da kudurin yadda ya kamata, da fadada taimakon jin kai, da samar da hanyar sanya ido nan da nan. A cewar masu fashin baki, matakin na kasar Sin bai zo da mamaki ba, duba da irin matakai da shawarwarin da take bayarwa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, wajen ganin an kawo karshen duk wani tashin hankali dake faruwa a sassan duniya. Har kullum kasar Sin na matukar adawa, tare da yin tir da dukkanin wasu hare-haren da ake kaiwa fararen hula.

Sanin kowa ne cewa, tsagaita bude wuta shi ne abu mai muhimmanci da ake bukata. Kuma kasar Sin ta jaddada kudurinta na yin hadin gwiwa da dukkan bangarori masu kaunar zaman lafiya wajen inganta hadin gwiwa, da daukar managartan matakai don kawo karshen tashe-tashen hankula a zirin Gaza, da aiwatar da shawarwarin kafa kasashen biyu, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gabas ta tsakiya. Wannan ya kara tabbatar da aniya da burin kasar Sin mai kaunar zaman lafiya, na gina duniya mai kwanciyar hankali da kowa zai ji dadin zama a cikinta. Sabanin yadda wasu kasashe ke kara rura wutar tashin hankali, ta hanyar nuna goyon baya ga wani bangare, domin cimma muradunsu na kashin kai, ba kuma tare da la’akari da yadda sakamakon hakan zai haifar ga fararen hula da ma kokarin da ake ba dare ba rana na neman wanzar da zaman lafiya a duniya ba. Amma kowa ya yi na gari don kansu. (Ibrahim Yaya)