Yawan yara kanana dake aiki ba bisa ka’ida ba ya karu a Amurka
2023-12-27 10:58:23 CMG Hausa
A jiya ne, kamfanin watsa labarai na CBS dake kasar Amurka ya bayyana cewa, yara kanana dake aiki a kamfanonin Amurka sun fi fuskantar barazanar rasa rayukansu sakamakon hadurran aiki, a gabar da karin yara da matasa a sassan Amurka ke gudanar da ayyuka masu hadari, wadanda ya kamata baligai su rika gudanarwa.
Bisa sakamakon bincike guda 955 da ma’aikatar harkokin kwadago ta Amurka ta gudanar a shekarar 2023, yawan lamurin hayar ma’aikata yara ba bisa doka ba ya karu da kashi 14 cikin dari, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na bara. Cikin shekara guda kafin ranar 30 ga watan Satumban bana, yawan yaran da suka yi aiki ba bisa doka ba ya karu da kashi 88 cikin dari bisa na shekarar 2019.
CBS ya bayyana cewa, sakamakon shigowar masu kaura da dama ba bisa doka ba a shekarun baya-bayan nan, musamman yaran dake shiga Amurka ba tare da iyayensu ba, kana da karancin ba da kariya ga ma’aikata yara a wasu jihohin Amurka, ya sa yawan ma’aikata yara a Amurka ya ci gaba da karuwa, kuma karin yara suna shiga ayyuka masu hadari. (Zainab)