logo

HAUSA

Rundunar sojin Najeriya: Dole a dauki kwararan matakin dakile ’yan ta’adda da masu tada kayar baya

2023-12-27 09:58:53 CMG HAUSA

 

Sakamakon karuwar hare-haren ta’addanci da ayyukan masu tada da kayar baya a sassan kasar daban daban, rundunar sojin Najeriya ta fito da sojoji dubu 50 domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma .

Babban hafsan sojin Najeriya Luftanant Janaral Taoreed Lagbaja ne ya tabbatar da hakan ranar Talata 26 ga wata a barikin soji na Giginya dake Sokoto lokacin da yake gudanar da bikin Kirismeti da dakarun tsaron musamman na Operation Hadarin Daji.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.