Karancin barci na illanta kwarewar yara wajen yin karatu
2023-12-27 08:41:14 CMG Hausa
Masu karatu, musamman ma dalibai, yau zan tunatar da ku dangane da muhimmancin yin barci isasshe.
Wani sabon nazari ya nuna cewa, idan daliban jami’a ba sa barci isasshe, wato tsawon lokacin barci bai kai awoyi 6 a ko wane dare ba, to, hakan na illanta kwarewarsu ta yin karatu.
Da ma dai wasu nazarce-nazarce sun shaida cewa, barci, muhimmin batu ne da ake yin la’akari da shi wajen kimanta lafiya, da kuma yadda ake aiki ko karatu. Nazarce-nazarcen da aka gudanar kan dabbobi sun nuna cewa, abubuwan da ake rikewa a kwakwalwa a rana za su samu ingantuwa a lokacin da ake barci. Idan an samu tsaiko ga yadda a kan yi barci, to, hakan zai haifar da saurin manta abubuwan da aka koya a rana. Masana sun bai wa matasa da kananan yara shawarar cewa, kamata ya yi su yi barci na tsawon awoyi 8 zuwa 10 a ko wane dare. Amma duk da haka, daliban jami’a masu yawa ba sa barci yadda ya kamata, wato ba sa barci isasshe.
Masu nazari daga jami’ar Carnegie Mellon ta kasar Amurka, da sauran hukumomi, sun gudanar da nazari kan dalibai fiye da dari 6 na ajin farko a jami’o’i 3. A ko wane dare, wadannan dalibai sun sanya na’urar binciken barci don sa ido da rubuta yadda suke barci. Masu nazarin sun tattara makin da daliban suka samu a karshen lokacin karatu na ajin farko, don kimanta illar da tsawon lokacin barci ke kawo wa karatunsu.
Masu nazarin sun gano cewa, matsakaicin tsawon lokacin barcin wadannan daliban jami’a ya kai awoyi 6 da rabi a ko wane dare. Idan tsawon lokacin barcinsu bai kai awoyi 6 ba, to, makin da suke samu a karatu zai ragu sosai. Idan kuma tsawon lokacin barcinsu ya karu da awa 1, to, matsakaicin makin da suke samu a karshen lokacin karatu zai dan karu.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, barci yana da matukar muhimmanci wajen yin karatu, da kuma rike abubuwa. Kaza lika karancin barci kan illata kwarewar daliban jami’a wajen yin karatu. Dangane da wannan, madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta yi mana karin haske da cewa, idan tsawon lokacin barci bai kai awoyi 6 ba a cikin dogon lokaci, hakan zai illata lafiyar mutum sosai. Don haka wajibi ne matasa, da kananan yara su sa muhimmanci kan yin isasshen barci a duhun dare. (Tasallah Yuan)