logo

HAUSA

Yadda Sin take kokarin bunkasa tattalin arziki na zamani

2023-12-27 07:24:50 CMG Hausa

A kwanakin nan ne, kasar Sin ta fitar da wani shiri game da aiwatar da ayyukan samar da wadata ta bai daya ta hanyar bunkasuwar tattalin arziki na zamani

Shirin wanda ofishin kididdiga da hukumar raya kasa da yin kwaskwarima suka fitar, na da nufin saukaka zurfafa hadewar fasahohin zamani da sashen samar da hidima da kayayyaki tare da magance matsalar rashin daidaito da rashin ci gaba ta hanyoyin zamani.

Kasar Sin ta sanya tattalin arzikin zamani ko na intanet ya zama muhimmin bangare na dabarun raya kasa. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 game da habaka Tattalin Arziƙi na Dijital, ya tanadi cikakken taswira da matakan habaka wannan fanni. A karkashin shirin, kasar Sin za ta kara karfinta a "bangarorin dabaru", kamar na'urori na zamani, runbun adana bayanai, sadarwa, da kuma kokarin samar da fasahohi kamar 6G. Har ila yau, tsarin zai sauƙaƙa tsarin samar da kayayyaki bisa sauye-sauyen zamani, don yin amfani da albarkatun bayanai da inganta tsarin tafiyar da tattalin arzikin intanet.

Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, ya kuma amince da manufar da za ta ƙara yawan muhimman masana'antu a fannin tattalin arzikin zamani zuwa kashi 10 na GDPn kasa nan da shekarar 2025, daga kashi 7.8 cikin 100 a shekarar 2020. Wannan adadi yana nufin ƙara darajar kai tsaye na musayar bayanai, manhaja, da hidima na fasahar bayanai. 

Ana fatan nan da shekarar 2025, za a samu ci gaba mai kyau wajen cike gibin dake tsakanin yankuna, birane da karkara, da kungiyoyin jama'a daban-daban da kuma a muhimman ayyukan jama'a ta hanyar bunkasa tattalin arzikin zamani.

Bugu da kari, nan da shekarar 2030, ana fatan samun gagarumin ci gaba wajen inganta ci gaban jama'a ta hanyar tattalin arziki na zamani, tare da sabbin tsare-tsare kan hadin gwiwa tsakanin yankunan gabashi da yammacin kasar.

Shirin ya yi tanadi kan muhimman abubuwa guda hudu, wadanda suka hada da inganta hadin gwiwar ci gaban yanki ta hanyar tattalin arziki na zamani, inganta ci gaban fasahohin zamani a yankunan karkara, inganta kwarewar jama’a a fannin fasahar zamani don samun aiki mai inganci, da saukaka samar da hidima a tsarin zamantakewa ta hanyar fasahohin zamani. (Ibrahim, Saminu, Sanusi Chen)