logo

HAUSA

Gibrima Abdullahi Maina: Kasar Sin tana saukaka wa baki ‘yan kasashen waje hanyoyin bude kamfaninsu a kasar

2023-12-26 15:57:38 CMG Hausa


Gibrima Abdullahi Maina, haifaffen Kanon tarayyar Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake gudanar da harkokin kasuwanci a birnin Guangzhou na kasar Sin.

A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Gibrima ya ce duk da cewa bai dade da fara kasuwancinsa a kasar Sin ba, amma ya fahimci manufofin gwamnatin kasar ga baki ‘yan kasashen waje, wadanda ke sha’awar zuba jari a kasar, kuma a cewarsa, manufofin suna taimakawa sosai wajen saukaka hanyoyin bude kamfanoni a kasar.

Malam Gibrima ya ce ta hanyar gudanar da hadin-gwiwa tare da kamfanonin kasar Sin, ya karu sosai a harkokin kasuwanci. Haka kuma ya bayyana wasu hajojin da kasar Sin take kerewa, wadanda ke jawo hankali da sha’awa sosai daga masu sayayya ko masu zuba jari na kasashe daban-daban.

A karshe, malam Gibrima ya bayyana fatansa ga shekara mai kamawa wato 2024. (Murtala Zhang)