logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen Masar da Iran sun tattauna kan halin da ake ciki a Gaza da yaki ya daidaita

2023-12-26 10:23:50 CMG Hausa

A jiya ne, ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry da takwaransa na Iran Hossein Amir-Abdollahian suka tattauna game da halin da zirin Gaza ke ciki da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, ministocin biyu sun yi musayar ra'ayi da nazari kan tabarbarewar yanayin jin kai da tsaro a yankin Falasdinu.

Sanarwar ta ce, sun kuma tsara hanyoyin da za a yi amfani da su wajen ganin an hada kai da kasashen duniya, don sassauta wa Falasdinawan radadin da suke fama da shi.

Kididdigar baya-bayan nan da ma'aikatar lafiya ta Gaza ta fitar jiya Litinin na nuna cewa, adadin Palasdinawa da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila ya kai 20,674, yayin da wasu dubu 54 da 536 suka samu raunuka, tun bayan barkewar rikici a ranar 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu. (Ibrahim Yaya)