logo

HAUSA

Hadarin mota ya hallaka mutane 11 a arewacin Najeriya

2023-12-26 10:24:46 CMG Hausa

Rahotanni daga arewacin Najeriya na cewa, mutane 11 ne suka mutu a ranar Asabar, bayan da wasu motoci biyu da suke ciki suka yi taho-mu-gama.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Jigawa, Lawal Shisu, ya bayyana cewa, dukkan mutanen dake cikin motocin biyu sun mutu nan take, bayan da motocin suka yi taho-mu-gama a Kwanar Gujungu dake karamar hukumar Taura a jihar Jigawa. Ya kuma dora laifin hadarin da mummunan gudun da direbobin motocin biyu suke yi.

Ana yawan samun munanan hadurra a titunan Najeriya, wanda galibi ke faruwa sakamakon lodin da ya wuce kima, da rashin kyawun titi, da kuma tukin ganganci. (Ibrahim Yaya)