logo

HAUSA

Sama da mutane 100 ne suka rasa rayukan su yayin wani hari da aka kai wasu kananan hukumomi 3 a jihar Filato

2023-12-26 09:07:40 CMG Hausa

Wasu ’yan ta’adda sun afkawa al’umomin yankunan kananan hukumomin Mangu da Bokkos da kuma Barkin Ladi a jihar Filato dake arewa ta tsakiyar Najeriya, inda  kusan sama da mutum 100 suka rasa rayukansu yayin da kuma  kaddarori da dama suka salwanta.

Al’amarin dai ya faru ne a jajiberin ranar bikin Kirsimeti, wanda ya yi sanadin daruruwan mutane barin muhallansu.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Farko dai ’yan ta’addan sun fara kai hari ga yankin Bokkos kafin daga bisani ya yadu zuwa wasu sassan yankin Barkin Ladi da Mangu.

A kalla dai ya zuwa yau Talata adadin mutanen da suke kwance a asibiti ya haura dari 3 bayan mumunan raunikan da suka samu yayin harin.

A lokacin da ya ziyarci yankunan da al’amarin ya faru da yammacin jiya Litinin, gwamnan jihar Filato Mr. Caleb Mutfwang ya yi alla wadai da wannan hari.

Ya ce ya kadu sosai da samun wannan labarin wanda ya yi sanadin mutuwar mutanen da ba su ji ba su gani ba a dai dai lokacin da ake tsaka da shagulgulan bikin Kirsimeti.

“Ina son na nanata cewa al’amarin ya isa haka, ba za mu taba amincewa da ci gaba da irin wannan halayya ta rashin hankali da rashin tunani ba na hare-haren babu gaira babu dalili, wannan abun takaici ne kuma abun kaico.”

Yayin ziyarar dai, gwamnan na jihar Filato yana tare ne da kwamandan rundunar Operation Save Heaven Major Janar Abdullsalam Abubakar. Kwamandan ya ce dakarun rudunarsa sun sami nasara fatattakar maharan, inda a lokacin suka sami nasarar samun wasu wayoyin hannun maharan.

“Ba za mu huta ba har sai mun kamo wadannan ’yan ta’adda, wanda yanzu haka wayoyin da muka samu sun fara ba mu haske a kan yadda za mu kamo masu laifin domin dai fuskantar hukunci.”

Yanzu haka dai an baza jami’an tsaro a yankunan guda uku, kuma tuni aka fara gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin tagwayen hare-haren. (Garba Abdullahi Bagwai)