logo

HAUSA

Iraqi ta yi tir da harin jirgi maras matuki da aka kai sansanin sojin Amurka dake arewacin kasar

2023-12-26 14:20:13 CMG Hausa

Gwamnatin Iraqi, ta yi tir da wani harin bam da aka kaddamar ta amfani da jirgin sama maras matuki, kan sansanin dakarun hadin gwiwa na sojojin saman Amurka, dake kusa da filin jirgin saman Erbil, na yankin Kurdistan mai kwarya-kwarya cin gashin kai dake arewacin kasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, kakakin rundunar sojojin kasar Iraqi Yahya Rasoul, ya ce harin ya raunata mutane da dama, ya kuma shafi ayyukan tashi da saukar jiragen sama a filin jirgin Erbil. Yahya Rasoul ya ce hari ne na ta’addanci, kuma masu son illata moriyar Iraqi ne suka kitsa shi.

Tun a jiyan ne kuma wata kungiya ta ‘yan gwagwarmayar Islama mai suna "Islamic Resistance in Iraq", ta fitar da sanarwar daukar alhakin kaddamar da harin, ta kuma ce ta kaddamar da wani harin bam na daban a sansanin sojojin Amurka na “Green Village”, wanda ke filin hakar mai na al-Omar dake kasar Syria.

Sanarwar kungiyar ta ce harin da dakarun ta suka kaddamar a Iraqi, martani ne cikin jerin matakan ramuwar gayya da take dauka kan dakarun sojin Amurka, a gabar da ake ci gaba da dauki ba dadi a zirin Gaza. (Saminu Alhassan)