logo

HAUSA

An ceto mutane 66 da aka yi garkuwa da su a jihar Sakkwato

2023-12-25 10:25:41 CGTN HAUSA

 

A karshen makon jiya ne runduna ta 8 ta sojojin Najeriya ta mikawa gwamnatin jihar Sokoto adadin mutane 66 da aka ceto daga hannun ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Kwamandan rundunar Birgediya Janaral Amos Tawasimi ne ya jagoranci mika mutane a wani kwarya-kwaryar biki da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar ta Sakkwato.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.