logo

HAUSA

Bai Jiajia: Ina son kowa ya ga fara'ar kasar Sin da damar da take samarwa duniya

2023-12-25 18:59:38 CMG Hausa

Bai Jiajia da har yanzu ke neman digiri na biyu a fannin koyar da Sinanci ga daliban kasashen ketare a jami’ar Huaqiao ta Xiamen, shekaru 6 ke nan da ta zo kasar Sin daga Indonesiya, kuma a yanzu ba magana da Sinanci kadai take yi ba, har ma da karanta wakar "Tunanin Dare " ta mawakin Daular Tang Li Bai. Da take waiwaye, na rashin sanin ta a lokacin da ta zo kasar Sin ba da dadewa ba, Bai Jiajia ta yi murmushi ta ce, sauraron yadda abokai Sinawa ke magana da Sinanci a lokacin, kamar sauraron "littattafai daga sama" ne.

"Kafin in zo kasar Sin, ina iya fahimtar Sinanci kadan. Amma, bayan na zo nan, lokacin da na yi magana da abokai na Sinawa, Sinancin da na ji a kunne na sun kasance kamar ‘ba la la la la’. Don haka lokacin farko da na iso kasar Sin, ba na iya fadar komai sosai sai sallama da murmushi."

Don haka, Bai Jiajia ta yanke shawarar koyon Sinanci sosai, kuma tana son ta iya jin Sinanci sosai kamar Sinawa. Don haka, a cikin shekarar farko bayan zuwanta kasar Sin, ta yi ta sa kaimi ga shiga cikin ayyukan makaranta da na cibiyarsu, hakan ya sa ta samu karin damammaki na yin mu’amala da Sinawa. Wani lokaci ba ta iya bayyana wani abu cikin Sinanci, don haka sai ta kwatanta da jikin ta, ko kuma ta yi amfani da harshen Indonesiya ko Turanci a maimakon Sinanci, malamai da abokan karatun ta na taimaka mata ta fadin kalmomin da take son furtawa, sannan su yi hakuri su koya mata yadda za ta bayyana ra’ayoyinta.

A cikin shekaru 6 da suka gabata, karkashin kwarin gwiwa da taimako daga malamai da abokan karatunta, Bai Jiajia ta shiga cikin wasu kungiyoyin makarantu, kamar su kungiyar matasan kasa da kasa dake cimma burinsu a kasar Sin, da kungiyar ba da hidima ta sa kai ta yada al'adun kasar Sin a ketare da dai sauransu. A shekarar 2020, ta kuma shiga ayyukan kafa kungiyar samar da gajerun bidiyo mai suna "Sabuwar Murya ta Ketare" don gogewa, da yin rikodin na fitattun labarun da suka faru a kasar ta Sin ta hanyar daukar gajerun bidiyo.

"A cikin shekaru shida a nan kasar Sin, na ga sauye-sauye da yawa a kasar. Akwai wanda yake burge ni sosai da ake kira ‘farfado da karkara’. "

Bai Jiajia ta ce, ta taba zuwa kauyuka da yawa a kasar Sin, inda ta ga mazauna kauyuka da yawa suna sayar da kayayyakin amfanin gona ta hanyar watsa shirye-shirye kai tsaye ta yanar gizo, a ganin ta, wannan abu ne mai kyau kwarai.

A wancan lokacin ita da abokan karatunta na kasashen waje sun yi gwajin kawar da talauci ta hanyar sayar da kayayyaki kai tsaye a yanar gizo, kuma dukkansu sun ji cewa, hada kasuwanci ta yanar gizo da farfado da karkara, wata hanya ce mai inganci sosai, wanda kuma ta kasance abin koyi ga sauran kasashe. A cewar Bai Jiajia, yana da ban mamaki yadda gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da irin wannan hanyar yin kirkire-kirkire, wajen farfado da yankunan karkara da kawar da talauci.

Gajerun bidiyon da Bai Jiajia ta dauka, ba wai sun yi rikodin labarai na gaskiya da ban al'ajabi da ke faruwa a kyawawan yankunan karkara a kasar Sin ba ne, har ma sun nuna kokarin da tsofaffin 'yan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke yi na neman alheri ga jama'a.

Bai Jiajia ta bayyana cewa, kasashen Sin da Indonesiya kasashe ne biyu dake da makwabtaka da juna. Babbar hanyar mota a tsakanin Medan da Kualanamu, da jirgin kasa mai saurin gaske a tsakanin Jakarta da Bandung, sun karfafa abokantaka tsakanin kasashen biyu. Baya ga haka, aikin gina yankunan hadin gwiwar masana'antu tare a tsakanin kasashen biyu, ya kara bunkasa mu’amala, da zuba jari ga juna tsakanin Indonesiya da Sin. Wadannan ayyukan za su cimma jerin nasarori, sakamakon karuwar hadin kai a tsakanin bangarorin biyu.

"Babbar hanyar mota a tsakanin Medan da Kualanamu, da jirgin kasa mai saurin gaske a tsakanin Jakarta da Bandung sun shahara a kasar Indonesiya, wadanda kuma suka nuna yadda kasar Sin ke samun saurin bunkasa a fannin fasahohi. "

Bai Jiajia ta kara da cewa, a ganinta, aikin gina yankunan hadin gwiwar masana'antu tare a tsakanin kasashen biyu, zai taimaka wajen kara hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki, da ma yin cudanya a fannin al’adu. Baya ga haka, zai ingiza kasar Indonesiya wajen neman ci gaban tattalin arziki, da samun guraban ayyukan yi. Ta ce, yanzu a kasar Indonesiya, mutanen dake fatan koyon Sinanci da fahimtar kasar Sin na kara karuwa, hakan ma dalili ne da ya sa take son zama wata malama mai koyar da Sicanci.

Duk lokacin hutun hunturu da na bazara, Bai Jiajia tana komawa birnin Medan na kasar Indonesiya, don koyar da yaran dake wurin yaren Sinanci, da ba su wasu darussa game da al'adun kasar Sin.

Sauyawar matsayinta daga daliba zuwa malama, ya sanya Bai Jiajia kara fahimtar kasar Sin a dukkan fannoni, kuma tana kara nuna kauna ga wannan kasa.

"Yaran suna sha'awar Sinanci sosai, ko da yake ba su san Sinanci kwata-kwata ba, amma ta hanyoyin koyarwa masu ban sha'awa, yaran suna samun saukin fahimta.”

Bai Jiajia ta ce, har ma wasu dalibai da dama suna cewa Sinanci ba ya da wahala ko kadan, kuma dole ne su yi aiki tukuru domin koyon Sinanci. Wasu yara har su kan ce mata, "Malama idan na girma, ina so in je kasar Sin don yin karatu kamar yadda kike yi."

Bai Jiajia ta gaya mana cewa, ta yi farin ciki sosai bayan ta ji haka, tana jin cewa ta zo kusa da cimma burinta, tana son kowa ya ga fara'ar kasar Sin, da damammakin da kasar ke samarwa duniya, kuma tana son taimakawa mutane da yawa su koyi Sinanci, da kusantar kasar Sin, da sanin kasar Sin, da ma kara fahimtar kasar Sin a dukkan fannoni. "