logo

HAUSA

Kasashen Duniya Na Kara Zuba Jari A Kasar Sin

2023-12-25 17:12:19 CMG Hausa

Yayin da kasar Sin ta samu bunkasuwar zuba jari daga ketare a wannan shekarar dake daf da karewa, kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suna ci gaba da yin amfani da tsofaffin dabaru wajen sukar yanayin kasuwanci da tattalin arzikin kasar Sin.  

Idan kana bibiyar sabbin labarai kan tattalin arzikin kasar Sin ko jarin waje a shafukan yanar gizo na kafofin watsa labaru na kasashen yamma, na tabbata za ka gano wasu labarai marasa dadi game da yanayin tattalin arzikin kasar ko kuma jarin waje.

Maganar gaskiya ita ce yawancin wadannan labarun ba daidai ba ne. Kasar Sin ta inganta yanayin kasuwancin kasar akai-akai tun farkon shekarar 2023 lokacin da ta bullo da matakai da dama don daidaita zuba jarin waje, wanda ya jawo karin kamfanonin waje zuba jari a kasar Sin, wanda kuma ke nuni da yadda tattalin arzikin Sin ke kara bunkasuwa cikin sauri.

Wani bincike da Faransa ta gudanar ya nuna cewa, yadda kasar Sin ta kara yawan jarinta na waje kai tsaye wato FDI, ya kara wa masu zuba jari kwarin gwiwa game da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, lamarin da ya sa wasu manazarta ke hasashen cewa, kamfanonin kasa da kasa sun yanke shawarar "karfafa kasuwancinsu a kasar Sin”, a cewar wani binciken da hukumar hidimar kudi wato "BNP Paribas Asset Management" ta Faransa ta yi.  

Kasar Sin ta zama cibiyar zuba jarin kasashen waje saboda yanayin tattalin arzikinta dake maraba da kamfanonin kasashen waje. Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2023, an kafa sabbin kamfanoni 41,947 da suka zuba jari a kasashen waje, lamarin da ya nuna babban ci gaban da aka samu da kashi 32 cikin 100 na jarin waje kai tsaye (FDI). FDI cikin kasar Sin ya karu da kashi 110.3, kashi 94.6, kashi 90, kashi 66.1, da kashi 33 cikin dari daga kasashen Canada, Birtaniya, Faransa, Switzerland, da Netherlands bi da bi. Wannan karuwar na da nasaba da yadda kamfanoni na kasa da kasa suke son zuba jari a kasar Sin.

Bugu da kari, jarin waje da fannin masana'antu ya samu ya kai Yuan biliyan 283.44 na kasar Sin, wanda ya nuna karuwar kashi 1.9 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Na'am, wannan labari ne mai ban sha'awa, la’akari da munanan bayanai da wasu kafafen yada labarai na kasa da kasa ke yadawa game da daidaituwar tattalin arzikin kasar Sin. Bayanan nasu ba su da tasiri yayin da saka hannun jari na yau da kullun na kamfanonin ketare ke karuwa. (Muhammed Yahaya)