Faransa ta sanar da rufe ofishin jakadancinta da ke Nijar
2023-12-25 10:19:42 CGTN HAUSA
Dangantaka tsakanin Nijar da Faransa ta kai karshen bango, bayan da a wannan mako a cikin wata sanarwa ta ranar 19 ga watan Disamba wacce ta tabbatar da rufe ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Yamai na jamhuriyar Nijar. Matakin da ya turo ’yan Nijar da dama masu bada hidima a ofishin jakadancin rasa aikinsu.
Daga birnin na Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya duba wannan batu ga kuma rahoton da ya aiko mana.