logo

HAUSA

Rikici ya haddasa mutuwar mutane 16 a Najeriya

2023-12-25 10:30:57 CMG Hausa

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mutane 16 ne suka mutu, a wani rikici da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a kauyen Mushu na jihar Filato da ke yankin arewa ta tsakiyar kasar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya ruwaito wani jami'in sojan Najeriyar na cewa, an kai harin ne da tsakar daren ranar Asabar, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin zubar da jinin.

Rundunar ‘yan sanda da jami’an tsaro, sun garzaya wurin da lamarin ya faru, domin dakile ta’azzarar rikici a yankin da ake yawan samun rikicin kabilanci da na addini. (Ibrahim)