logo

HAUSA

Kimiyya Da Kwaskwarima Suna Sa Kaimin Zamanintar Da Aikin Noma A Kasar Sin

2023-12-25 16:41:42 CMG HAUSA

DAGA MINA

Kasar Sin babbar kasa ce a fannin noma, ganin yadda yawan manomanta ya kai miliyan 700, wanda ya kai kashi 50.1% na dukkan jama’ar kasar. Hakan ya sa, aikin gona da raya kauyuka, da manoma, sun zama muhimman batutuwa uku dake shafar bunkasuwar tattalin arziki, da zaman karkon al’umma da wadatar kasar. Saboda hakan, jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin (JKS) da ma gwamnatin kasar suna mai da hankali matuka kan wadannan batutuwa, kuma kwamitin kolin jam’iyyar ta kan kira taro kan ayyukan raya kauyuka a karshen kowace shekara, don a tattauna halin da ake ciki da kalubalolin da ake fuskanta ta wadannan fannoni uku, tare da tsara shirin ayyuka da za a aiwatar a shekara mai zuwa.

Kwanan baya, kwamitin kolin JKS ya kira taro kan raya kauyuka a nan birnin Beijing, inda a gun taro, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nanata wajibcin kafa madaidaitan ra’ayoyin aikin gona da na abinci, inda ya kamata a raya aikin noma, da kiwon dabobbi da kamun kifi tare, ta yadda za a kafa wani tsarin samar da abinci iri daban-daban.

Madaidaicin ra’ayin raya aikin gona shi ne raya aikin gona bisa fasahohin zamani, wato a gudanar da ayyukan gona ta hanyar amfani da fasahohin zamani da kayan aikin da aka samar bisa bunkasuwar masana’antu na zamani.

Bisa kididdigar da aka fitar, an ce tun lokacin da aka kammala babban taron wakilan jam’iyyar JKS karo na 18 a shekarar 2012, kason ayyukan gona da aka gudanar ta yin amfani da injunan zamani ya karu daga kashi 57% zuwa kashi 73% a shekarar 2022, kana yawan gudunmawar da kimiyya ta bayar a fannin aikin gona ta karu daga kashi 54.5% a 2012 zuwa kashi 62.4% a 2022.

Kimiyya da fasaha na ingiza zamanintar da aikin noma a kasar Sin. A shekarar da muke ciki, duk da bala’u daga indallahi da dama da aka fuskanta, amma kasar Sin ta yi girbi mai armashi, hakan ya sa Sin ta kiyaye yawan hatsin da ta samar a sama da kilogiram triliyan 6.5 cikin shekaru 9 a jere. Muna iya ganin cewa, kimiyya da kwaskwarima sun sa kaimin zamanintar da aikin noma, kuma sun ba da tabbaci ga aikin zamanintar da kasar Sin. (Mai zane da rubutu: MINA)