logo

HAUSA

Bude Kofa Da Cin Moriya Tare: Kasashen Afrika Na Cin Gajiyar Tsarin Yin Kwaskwarima Da Bude Kofa Da Gwamntin Sin Ke Dauka

2023-12-25 16:39:46 CMG HAUSA

DAGA MINA

A yankin Asokoro na birnin Abuja hedkwatar kasar Najeirya, inda jami’an ofisoshin jakadancin kasashe daban-daban da jami’an gwamantin kasar suke zaune, akwai wani titi mai suna “Titin Deng Xiaoping”. Marigayi Deng Xiaoping mai jagorancin tsarin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga wajen da gwamnatin Sin ta dade tana daukawa, an nadawa wani titi sunansa, muna iya ganin cewa, ci gaban da aka samu karkashin wannan tsari na burge jama’ar wurin.

Me ya sa, idan an duba wasu ayyukan more rayuwa da kamfanonin Sin suka ba da taimako wajen gudanarwa, sun kasance sakamakon wannan tsari na hadin kai. Alal misali layin dogo dake tsaknian Abuja da Kaduna, tashar ruwa mai zurfi ta Lekki, da sabon titin filin saukar jiragen sama na Abuja, da madatsar ruwa ta Zungeru da sauransu, ana iya gani irin wannan aiki a fadin nahiyar Afrika.

Bana ake cika shekaru 45 da aiwatar da wannan babban tsari, kuma ci gaban da S    in ta samu na a zo a gani, da bude kofarta ga kasashen waje da gwamnatin Sin ke daukakawa na haifar da ci gaban kasashen Duniya, musamman ma kasashen Afrika.(Mai zane da rubutu: MINA)