Wani hari ta sama da sojojin Isra’ila suka kaddamar kan sansanin ’yan gudun hijira dake tsakiyar Gaza ya hallaka a kalla mutum 70
2023-12-25 10:24:30 CGTN HAUSA
Rahotanni daga gidan talabijin mallakin Falasdinu, na cewa a kalla Falasdinawa 70 ne suka rasu, sakamakon wani hari ta sama da dakarun sojin Isra’ila suka kaddamar kan sansanin ’yan gudun hijira na al-Maghazi, wanda ke tsakiyar zirin Gaza.
Wata sanarwar da kakakin hukumar lafiya dake Gaza Ashraf Al-Qedra ya fitar, ta ce akwai yiwuwar adadin mamatan ya karu, sakamakon harin na jiya Lahadi, ya fada ne a yanki mai dandanzon al’umma.
A daya bangaren, yayin taron mako-mako na majalissar gudanarwar Isra’ila, firaministan kasar Benjamin Netanyahu, ya musanta rahotannin dake cewa Amurka ta hana kasarsa aiwatar da matakan soji a Lebanon. Netanyahu ya ce "Isra’ila kasa ce mai cin gashin kai. Muna aiwatar da matakan yaki ne bisa shawarwarin da muka yanke, kuma ba zan yi wani karin haske kan hakan ba. Rundunar tsaron kasarku IDF, ita ce ke da wuka-da-nama game da yanke hukuncin matakan da suka dace a aiwatar, ba wani bangare na daban ba."
Daga nan sai ya yi gargadin cewa, yakin ba mai karewa ne nan da nan ba. Kaza lika mista Netanyahu ya jaddada cewa, kammalar yakin na da alaka ne kai tsaye, da lokacin da suka kawar da Hamas, da kuma tabbatar da kubutar da wadanda ake tsare da su a Gaza. (Saminu Alhassan)