logo

HAUSA

Yan tawayen Houthi sun sake gargadin sojojin Amurka dake gabar tekun Bahar Maliya

2023-12-25 10:13:38 CMG Hausa

'Yan tawayen Houthi na kasar Yemen, sun sake sabunta gargadin da suke yiwa sojojin Amurka, inda suka bukaci da su gaggauta ficewa daga tekun Bahar Maliya kafin wurin ya zama fagen daga

Mai magana da yawun kungiyar, Mohammed Abdulsalam ya fada a wata sanarwa da tashar talabijin ta al-Masirah ta kungiyar ta watsa cewa, Bahar Maliya za ta zama fagen daga, idan har Amurka da kawayenta suka ci gaba da cin zarafin da suke aikatawa.

Gargadin na zuwa ne, a daidai lokacin da Amurka ta zargi 'yan Houthi da amfani da jirgi mara matuki, wajen kai wa wani jirgin ruwan danyen mai dake dauke da tutar kasar Indiya, mallakin kasar Gabon, mai suna MV Saibaba hari, zargin da Abdulsalam ya musanta, yana mai cewa, wani jirgin ruwan Amurka ne ya kai wannan hari da makami mai linzami a karshen kudancin tekun Bahar Maliya.

Abdulsalam ya kara da cewa, a yayin da wani jirgin saman sojan ruwanmu ke gudanar da aikin leken asiri a kan tekun Bahar Maliya, wani jirgin ruwan yakin Amurka ya bude masa wuta da makamai da dama. Ya kara cewa, daya daga cikin makamin ya tarwatse a kusa da MV Saibaba, wanda ya taso daga tashar jiragen ruwan kasar Rasha ya nufi kudu.

Kakakin ya yi Allah-wadai da harin da Amurka da kawayenta suka kai a tekun Bahar Maliya, yana mai cewa, suna barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa na kasa da kasa, da ma neman su fice. (Ibrahim)