logo

HAUSA

Me ya sa ya kamata a rungumi shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya

2023-12-24 18:38:45 CRI

Kayayyakin tarihi na garin Liangzhu da masu binciken kayan tarihi suka gano, a wani babban bincike da aka gudanar a kasar Sin a karni na 20, sun sake ja hankalin duniya, yayin da aka bude dandalin Liangzhu na farko a kwanakin baya a birnin Hangzhou, hedkwatar lardin Zhejiang. Wadannan kayayyakin tarihi da aka fara gano su a birnin Hangzhou a shekarar 1936, ya nuna wayewar kan noman shinkafar kasar Sin ta zamanin da, wanda ya kasance tsakanin shekarun 3300 da 2300 kafin haihuwar Annabi Isa, wanda ake daukarsa a matsayin wata kwakkyarar shaidar wayewar kan kasar Sin ta shekaru dubu biyar. Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, shahararren masanin huldar kasa da kasa da harkokin duniya daga jami’ar Abuja ta tarayyar Nijeriya na daga cikin wadanda suka halarci taron dandalin na Liangzhu.

A kasance tare da mu cikin shirin, don jin tattaunawar da muka yi tare da Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim.(Lubabatu)