Kasafin kudin ayyukan soji na kasashen Amurka da Japan ya karu zuwa wani sabon matsayi
2023-12-24 16:53:09 CMG Hausa
Kasashen Amurka da Japan, wadanda ke kan gaba wajen kashe makudan kudade a fannin ayyukan soji, sun bayyana aniyar kashe karin kudade a fannin, cikin kasafin su na shekarar 2024 dake karatowa, inda za su kafa wani sabon tarihi na karuwar kashe kudade a ayyukan soji.
A ranar Juma’a ne dai shugaban Amurka Joe Biden, ya sanya hannu kan kudurin dokar kasafin kudin kasarsa, mai kunshe da tanadin kashe dala biliyan 886 duk shekara a fannin ayyukan soji. Cikin kudurin na NDAA, mai kunshe da kusan shafuka 3,100, an ayyana karin kaso 5.2 bisa dari ga kudin da ake biyan jami’ai masu aikin soji, da karin jimillar kasafin kudin da ya shafi tsaron kasa da kaso kusan 3 bisa dari.
A nata bangare kuwa, Japan wadda a baya ke rungume da manufofin kundin tsarin mulkinta na bayan mika wuya bayan yakin duniya na 2, a yanzu ta fara sauya tafarki, inda take ta kara fadada fannin ta na ayyukan soji.
A ranar Juma’a, majalissar zartaswar kasar ta amince da kashe karin kaso 16 bisa dari a ayyukan sojin kasar a shekarar 2024, tare da sassauta matsayarta ta bayan yaki, dangane da hana fitar da makamai masu hadari, wanda hakan ke nuni ga yadda kasar ke ban kwana da manufofin ta na tsaron kai kadai. (Saminu Alhassan)