logo

HAUSA

Morocco da wasu kasashen yankin Sahel sun tattauna kan karfafa alaka a yankin su

2023-12-24 16:59:12 CMG Hausa

Ministocin harkokin waje ko wakilan kasashen Morocco, da na kasashen yankin Sahel da suka hada da Burkina Faso, Chadi, Mali, da Nijar, sun gudanar da wani taro a birnin Marrakesh dake kudancin kasar Morocco a jiya Asabar 23 ga wata, inda suka tattauna saukin da za a samu wajen hada kan kasashen yankin Sahel da tekun Atlantika, da ma karfafa sadarwa a tsakanin kasashen yankin.

Wannan taron daidaitawa, ya mayar da hankali ne kan shawarar da Sarki Mohammed VI na Morocco, wato Sidi Mohammed ya gabatar a baya.

A cewar sanarwar bayan taron da aka yi a jiya, mahalarta taron sun bayyana a cikin jawabansu cewa, shawarar da abun ya shafa, za ta taimaka wa kasashen da ba su da iyaka da teku a yankin Sahel, wajen hada kai da yankunan tekun Atlantika, ta yadda za a samar da damammaki na bunkasa tattalin arziki, da hada-hadar ababen more rayuwa a tsakanin su.

Kana kuma, dukkanin bangarorin da suka halarci taron sun amince da kafa rukunonin aiki na kasa a kasashensu, domin inganta tabbatar da shawarar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)