logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta ce cusa akidar kishin kasa a zukatan al’umma shi ne babban matakin da zai yi maganin matsalar tsaro a kasa

2023-12-24 15:28:36 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, kyautata sha’anin kishin kasa a zukatan al’umma na daya daga cikin manyan dabarun da za su dakile matsalolin tsaro da sauran ayyukan ta’addanci a kasa baki daya.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Alhaji Muhammed Idris ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa yayin ziyarar neman hadin kan kafofin yada labaru wajen yaki da ayyukan ta’addanci a sassan kasar daban daban.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan yada labarun na tarayyar Najeriya ya ce, sanin ’yancin kai da kishin kasa da kuma kaunar juna su ne matakai na farko da za a fara tabbatar da wanzuwarsu a tsakanin ’yan Najeriya muddin dai ana son a ci karfin ayyukan ta’addanci da sauran miyagun laifufuka a kasar.

Ministan ya bayyana jin dadinsa bisa ziyarar neman hadin gwiwa da ma’aikatarsa da kuma rundunar tsaron Najeriya wajen yaki da hare-haren ta’addanci, inda ya ce, kafofin yada labarai na da gagarumar rawar takawa ta fuskar wayar da kan jama’a game da kishin kasa da kuma illolin matsalar tsaro.

“Wajibi ne a dawo da ra’ayin kishi da kaunar kasa a zukatan al’umma muddin dai ana son tabbatuwar hadin kai da wadatar kasa.”

Ya ce duk mai kishin kasarsa ba zai taba yarda a samu wani tashin hankali ba.

A jawabinsa, babban hafsan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa ya ce, ziyarar da suka kaiwa ministan yana daga cikin matakan yaki da ta’addanci ta hanyar diplomasiyya ba tare da amfani da karfin tuwo ba, kuma amfani da kafofin labarai wajen karfafa zukatan ’yan kasa yana da matukar tasiri sosai, duk da cewa su ma ’yan ta’adda suna amfani da nasu kafofin wajen yada furofaganda domin sanya fargaba a zukatan mutane.

“A cikin tsarin aikinmu, samun bayanai na da matukar mahimmanci a gare mu.”

Janaral Christopher Musa ya nemi hadin kan al’umma, domin a cewarsa sai da hadin kan ’yan Najeriya za a iya maganin ayyukan ta’addanci wadanda ke haifar da kalubale ga ci gaba da tabbatuwar Najeriya a matsayin kasa mai ’yanci. (Garba Abdullahi Bagwai)