Iran ta gudanar da taron kasa da kasa na neman goyon bayan Falasdinawa
2023-12-24 17:16:35 CMG Hausa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, ta ce an shirya taron kasa da kasa na yini guda a jiya Asabar a birnin Tehran, domin nemawa falasdinawan dake Gaza da yamma da kogin Jordan goyon baya.
Cikin sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta ce taron ya mayar da hankali ne ga neman a janye shingen da aka kafa a Gaza, da tabbatar da samar da karin agajin jin kai ga mazauna yankuna masu makwaftaka da teku.
Taron wanda bangare ne na kokarin Iran ta fuskar diflomasiyya, na mara baya ga falasdinawa, ya samu halartar jami’ai, da ‘yan siyasa, da malaman addinai, da ‘yan jarida, da masana daga sama da kasashen duniya 50.
Shugaban Iran Ebrahim Raisi, na cikin wadanda suka gabatar da jawabi yayin taron, inda a cikin jawabinsa ya zargi Amurka da kasancewa a sahun gaba, wajen keta hurumin dimokaradiyya, yana mai kira gare ta, da ta kauracewa wani tunani na tsara makomar Gaza, domin makomar yankin na hannun al’ummun sa, da kuma halastattun gwamnatocin sa.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba da ya gabata kawo yanzu, jimillar Falasdinawa da Isra’ilawa da suka rasu, sakamakon yakin da ya barke a zirin Gaza, ya karu zuwa mutum 20,258, baya ga 53,688 da suka jikkata, kamar dai yadda ma’aikatar lafiya da ke Gaza ta tabbatar cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Asabar.
A wani ci gaban kuma, a dai jiyan, shugaban Amurka Joe Biden, ya zanta da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu. To sai dai kuma a cewar fadar White House ta Amurka, Biden ya ki ya bayyana cikakken abun da tattaunawar ta su ta kunsa, inda ya shaidawa manema labarai cewa "Tattaunawa ce ni da shi. Amma dai ban yi kira da a tsagaita wuta ba". (Saminu Alhassan).