Antonio Guterres ya yi maraba da kudurin kwamitin tsaro game da samar da kudaden ayyukan wanzar da zaman lafiya karkashin AU
2023-12-23 16:03:06 CMG Hausa
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da kudurin kwamitin tsaro majalisar, game da samar da kudaden gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya karkashin kungiyar tarayyar Afirka ta AU.
Cikin wata sanarwa da kakakin sa Stephane Dujarric ya fitar game da hakan, mista Guterres ya ce tun kama aikin sa a matsayin babban jami’in MDD, ya sha jaddada kira ga samar da sabon tsarin tallafawa ayyukan wanzar da zaman lafiya, karkashin jagorancin abokan hulda na nahiyar, tsarin da zai tabbatar da samar da isassun kudade na wanzar da zaman lafiya, da kalubalen tsaro a nahiyar. Ya ce hakan daya ne daga muhimman shawarwari dake cikin manufar baya bayan nan da ya gabatar karkashin sabuwar ajandar samar da zaman lafiya.
Sanarwar ta kara da cewa, kudurin zai taimaka wajen shawo kan babban gibi na tsawon lokaci da ake samu, a fannin shawo kan batutuwan zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, tare da ingiza kwazon sassan kasa da kasa wajen shawo kan matsalolin zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka. (Saminu Alhassan)