MDD ta sanar da bikin bazara na Sin a matsayin daya daga bukukuwan da za a rika kiyaye kimar su
2023-12-23 16:34:29 CMG Hausa
Bikin bazara na al’ummar Sinawa dake gudana bisa kalandar wata, ya shiga cikin jerin ranaikun hutu na MDD dake fadowa a ranaiku mabambanta, a jerin bukukuwa, da tarukan MDD tun daga shekarar 2024.
Cikin wani kuduri da aka gudanar a babban taron MDD, an amince da muhimmancin bikin bazara na Sin, wanda ake bikinsa a kasashe mambobin MDD da dama, don haka aka bukaci hukumomin MDD dake hedkwatar, da sauran cibiyoyin gudanar da ayyukan ta, da su rika gudanar da bikin ranar, domin kaucewa gudanar da taruka a ranar bikin sabuwar shekarar ta Sin.
Game da hakan, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya ce bayan amincewa da kudurin mai nasaba da bikin bazara na al’ummar Sinawa, a matsayinsa na bikin gargajiya na Sinawa dake mayar da hankali ga haduwar iyalai, da fatan alheri ga shekara mai kamawa, hakan ya shaida akidun wayewar kan kasar Sin mai kunshe da zaman lafiya da jituwa, tare da yayata akidun bai daya na bil adama, kamar zaman jituwar iyalai, da dunkulewar zamantakewa, da inganta alakar mutum da halittun da yake rayuwa cikin su.
Dai ya kara da cewa, kokarin Sin na yayata al’adun bikin bazara a matsayin ranar hutu ta MDD, muhimmin mataki ne na cimma manufar wayewar kai ta bil adama, da yayata banbance banbancen wayewar kai daban daban. Don haka kudurin ya shaida muhimmancin cudanyar al’adu daban daban, da tafiya tare don yayata manufofin MDD. (Saminu Alhassan)