logo

HAUSA

Kason karshe na Sojojin Faransa sun bar janhuriyar Nijar

2023-12-23 16:29:34 CMG Hausa

Rundunar sojojin janhuriyar Nijar ta bayyana a jiya Jumma’a cewa, kason karshe na sojojin kasar Faransa da suka rage a kasar sun fice, wato dai Faransa ta kammala aikin kwashe dukkanin sojojin ta da ta jibge a kasar. Kafin hakan a ranar 19 ga watan nan, ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fayyace a cikin wani sakon da ta tura wa ma’aikatan da ofishin jakadancinta dake Nijar ya yi hayarsu a kasar cewa, gwamnatin Nijar ta kayyade aikin diplomasiyyar ofishin, a sakamakon haka, a yanzu Faransa ta tsai da kudurin rufe ofishin. (Jamila)