logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya zartas da kudurin kara baiwa yankin Gaza taimakon jin kai

2023-12-23 16:57:02 CGTN HAUSA

 

Jiya Juma’a, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2720, da kuri’un amincewa 13, da na janyewa 2, wanda ya nemi kara baiwa yankin Gaza tallafin jin kai nan da nan, ba tare da ko wane shinge ba, ga fararen hula Palasdinawa, da kuma samar da sharadi mai kyau na watsi gaba da juna.

Kudurin ya nemi bangarorin da rikicin ya shafa da su bude hanyoyin da suka dace, da sakin mutanen da suke tsare da su, da biyan bukatun jiyyarsu, da kuma samarwa yankin makamashi da ake bukata a yau da kullum. Kudurin kuma ya nanata matsayin da kwamitin ya dauka, na goyon bayan tsarin “kafa kasashe biyu”, da muhimmancin dinkewar yankin karkashin mahukuntan Palesdinu.

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya bayyana bayan kada kuri’un cewa, Sin na maraba da kudurin da kwamitin ya zartas. Ya ce tsagaita bude wuta muhimmin mataki ne da aka sanya gaba. Kuma Sin na fatan hadin kai tare da sauran mambobin kwamitin, don ci gaba da ingiza matakan da suka wajaba, masu cike da ma’ana da kwamitin ya dauka, da taka rawar gani wajen tabbatar da an ajiye makamai, da gudanar da tsarin “kafa kasashe biyu”, da wanzar da zaman lafiya da karko a yankin Gabas ta Tsakiya. (Amina Xu)