Nagartar Tunanin Sinawa:Ba za a iya raba kasa ba, ba za a iya wargaza wayewar kai ba
2023-12-22 14:32:10 CMG Hausa
A bayyane yake cewa a tsohon tarihin dan Adam, ba safai ake samun kasa mai wayewar kai kamar Sin da ta iya kiyaye hadin kai na dogon lokaci ba.
Me ya sa wayewar kan Sin ba kawai ta ci gaba ba tare da katsewa ba, har ma ta kiyaye babban matakin hadin kai?
A kashi na uku na jerin shirye-shirye game da “Nagartar Tunanin Sinawa”, Fitaccen masanin kimiyyar siyasa farfesa Zhang Weiwei da mai gabatar da shirin, sun tattauna kan tarihin wayewar kan kasar Sin game da hadin kan mabambantan ra’ayi.