logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta kammala aikin gyaran matatar man dake Fatakwal

2023-12-22 09:10:46 CMG Hausa

 

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa, an kammala manyan ayyukan gyaran injunan dake kamfanin mai na Fatakwal, daya daga cikin tsoffin matatun tace man fetur a kasar.

Karamin ministan albarkatun man fetur na kasar Heineken Lokpobiri ne, ya shaidawa manema labarai hakan a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers mai arzikin man fetur. Yana mai cewa, wuta ya fara fita a matatar da ke da karfin tace ganga dubu 210 na danyen mai a kowace rana

Matatar mai ta Fatakwal, mai dauke da sassan tace mai guda biyu, an rufe ta ne a watan Maris din shekarar 2019, yayin kashi na farko na ayyukan gyaran matatar, a wani bangare na kudirin gwamnati na farfado da sabunta muhimman ababen more rayuwa. Ana sa ran aikin gyare-gyaren, zai bunkasa aikin tace mai a cikin gida da kuma rage dogaron da kasar ke yi kan man da ake shigowa da shi daga kasashen waje.(Ibrahim)