Bola Ahmed Tinubu: Babu batun yafiya ga wadanda suka yi sanadin harin bom a kauyen Kaduna
2023-12-22 09:32:13 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada cewa duk wanda yake da hannu a harin bom da aka kai kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna zai fuskanci hukunci mai tsanani da zarar sakamakon bincike ya fito.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Alhaji Mohammad Idris ne ya tabbatar da hakan a jiya Alhamis a birnin Abuja yayin wani taron manema labarai na duniya da ya gudanar domin bayyana nasarorin gwamnati a cikin watanni 7.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan yada labaran na tarayyar Najeriya ya ce, tuni aikin binciken hatsarin ya yi nisa sosai wanda nan gaban kadan ake sa ran fito da sakamako, wanda kuma za a sanar da ’yan Najeriya wadanda suke da hannu a harin da kuma nau’in hukuncin da za a yi musu daidai da dokar kasa.
Ministan ya ci gaba da cewa, gwamnatin ba za ta taba bari wasu ko kuma wani ya yi wa manufarta kan sha’anin tsaron kasa makarkashiya ba, koda yake ya ce, gwamnati na sane da kalubalen da bangaren tsaro ke fuskanta kama daga garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan ta’adda a sassa daban daban na Najeriya.
A kan haka ne ma a kasafin kudin cike gibi na wannan shekara da muke bankwana da ita, ministan ya ce, “Kaso mafi tsoka na Naira tiriliya 2.17 ya tafi ne ga bangaren tsaro, ha’ila yau kuma an samar da kaso mai yawa na kunshin kasadin kudin badi na 2024 ga sha’anin na tsaro, hakan ya zama wajibi domin a same damar daukar karin jami’an tsaro tare da ba su horo da sauran aikace-aikace.”
Babban abun da ake son cimmawa dai a cewar ministan shi ne samar da yanayin mai kyau da ’yan kasa za su rinka gudanar da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba a duk inda suke a kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)