logo

HAUSA

Wakilin Sin: Ya dace a daidaita batun kiyaye zaman lafiya na AU ta hanyoyin Afirka

2023-12-22 14:11:04 CMG Hausa

Mukaddashin shugaban tawagar wakilan kasar Sin dake MDD Dai Bing, ya ce game da yadda za a daidaita batun kiyaye zaman lafiya, da samar da kudade ga kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU, ya dace a bi manufar warware batutuwan dake gaban kasashen na Afirka ta hanyoyin Afirka.

A yayin da yake jawabi a jiya Alhamis, Dai bing ya ce bayan kada kuri’a kan daftarin kwamitin sulhun MDD, game da batutuwan kiyaye zaman lafiya da samar da kudade ga kungiyar AU, kasar Sin na maraba da zartas ta kudurin da kasashen Afirka uku suka gabatar wa kwamitin sulhun MDDr.

Kaza lika kasar Sin ta kada kuri’ar amincewa da daftarin, ta kuma halarci aikin gabatar da daftarin cikin hadin gwiwa. Har ila yau, Sin na fatan a nan gaba, a yayin da MDD ke goyon bayan AU kan ayyukan kiyaye zaman lafiya, za ta kuma bi ka’idar jagorancin Afirka da ’yancin Afirka.

Ya kara da cewa, bai kamata kasashe masu ci gaba, su rage taimakon kudi da suke samarwa aikin ba, kuma kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan kasashen Afirka, wajen warware matsalolin dake gabansu ta hanyoyin kansu, za ta kuma samar musu da taimakon kudi, da kayayyaki, domin kara karfinsu na gudnaar da ayyukan kiyaye zaman lafiya.

A sa’i daya kuma, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasashen duniya, wajen ba da karin gudummawa ta fuskar kare zaman lafiya, da zaman karko a nahiyar Afirka.  (Mai Fassarawa: Maryam Yang)